Gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta fara tilasta wa ‘yan jaridar kafafen yaɗa labarai na gwamnati da masu zaman kansu shiga horon soja na musamman domin ƙarfafa kishin ƙasa.
DWAfrica ta ruwaito rukunin farko na ‘yan jarida 44, maza da mata, sun kammala horon kwanaki shida a wata makarantar ‘yan sanda da ke kusa da Ouagadougou, inda aka gan su sanye da kayan sojoji rike bindigogi.
Gwamnati ta ce shirin na shekara-shekara na da nufin ƙarfafa kishin ƙasa yayin da ƙasar ke ci gaba da yaƙi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.