Rundunar ’yan sandan jihar Sakkwato ta ce jami’anta na musamman sun kashe ’yan bindiga biyu dauke da makamai, sun kwato bindigogin AK-47 guda biyu da harsasai, tare da kama wasu mutane da ake zargi da hannu a kungiyoyin satar babura a sassan jihar.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya fitar, rundunar ta ce wannan gagarumar nasara ta biyo bayan wasu samame da aka gudanar a ranar 14 da 15 ga watan Agustan nan, a wani bangare na kokarin dakile ’yan bindiga, satar babura da sauran ayyukan ta’addanci.
A cewar sanarwar, a ranar 15 ga watan Agusta, jami’an tsaro sun mayar da martani kan kiran gaggawa cewa wasu ’yan bindiga dauke da makamai sun fito daga dajin Tsauana domin kai hari kauyen Dankadu da ke karamar hukumar Illela.
’Yan sandan sun ce daga bisani jami’an tsaro sun ratsa dazuzzukan da ke kewayen yankin tare da kashe biyu daga cikin ’yan bindigar da suke tserewa, inda suka kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, harsashi biyu da kuma wasu harsasai 54.
Duk a wannan ranar, jami’an ’yan sanda sun kama wasu mutane uku da ake zargi da satar babura, wadanda aka bayyana sunayensu da Siba Abdullahi daga kauyen Dimbiso, karamar hukumar Wurno, Hassan Hassan na Tamaje da Usama Isah na Unguwar Rogo da ke Sakkwato.
An kwato babura biyar da aka sace da kuma bindiga kirar gida guda daya a yayin binciken maboyarsu da ke yankunan Kwannawa da Tamaje a cikin birnin Sokoto.