NE

News Elementor

Tinubu ya gana da shugaban EFCC da ministan gidaje domin tsara yadda za’a sayar da gidajen da aka ƙwace

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gana da schugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, EFCC, Ola Olukoyede, da Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane, Muttaqha Rabe Darma, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa taron ya mayar da hankali ne kan yadda za a gudanar da harkokin gidajen da EFCC ta ƙwace a faɗin ƙasar, da kuma yadda za a sayar da su bisa ƙa’idojin gaskiya da riƙon amana.

Ofishin yaɗa labaran fadar shugaban ƙasa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da hotuna da ya fitar a daren Talata.

Wannan ganawa ita ce ta farko da aka bayyana a bainar jama’a tsakanin Tinubu da Olukoyede tun bayan da shugaban ƙasar ya soke matakin EFCC na daskarar da asusun gwamnatin Jihar Osun a farkon watan nan, kwanaki kaɗan kafin zaɓen gwamnan jihar.

A ranar 5 ga Agustan 2026, EFCC ta samu umarnin kotu na daskarar da asusun gwamnatin Osun, tana mai cewa tana binciken yadda ake zargin an karkatar da wasu kuɗaɗen muhalli, kuɗaɗen tallafi da rabon kuɗaɗen tarayya da jihar ke samu, waɗanda adadinsu ya kai kusan naira biliyan 11.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM