NE

News Elementor

Fiye da mutane 3,000 sukabar gidajensu sakamakon hare-haren yan bindiga a jihar Katsina

Fiye da mutane 3,000 a Unguwar Guru da ke Unguwar Sukuntuni ta Ƙaramar Hukumar Kankia a Jihar Katsina, ne suka tsere daga gidajensu, kuma yanzu haka suna samun mafaka a gine-ginen da ba a kammala ba, makarantar firamare da kuma wajen ’yan uwa, sakamakon sabbin hare-haren ’yan bindiga.

Garin ya sha fama da hare-haren ’yan bindiga a cikin ‘yan kwanakin nan.

Sabbin hare-haren sun faru ne a ranar Asabar da Litinin, inda aka kashe mutane 13, sannan aka sace mata da ’yan mata da dama.

Mazauna garin da suka rasa matsugunansu, wadanda suka shafe fiye da kwanaki tara a kauyen Rimaye, sun shaida wa Daily Trust cewa sun bar gidajensu ba tare da kusan komai ba, kuma har yanzu ba su samu wani tallafi daga gwamnatin Jihar Katsina ko gwamnatin tarayya ba.

Muhammadu Lurwanu, wani mazaunin Unguwar Guru, ya ce an tilasta wa daukacin al’ummar garin wansa ke da mutane sama da 3,000, barin gidajensu bayan hare-haren.

Ya yi kira ga gwamnatin Jihar Katsina da ta gaggauta shiga tsakani tare da samar da abinci, tufafi, ruwa da sauran muhimman kayayyakin agaji ga mutanen da suka rasa matsugunansu.

Wani mazaunin garin, Yahaya Matsiga, ya bayyana halin da ake ciki a matsayin “mai matukar tsanani da tausayi,” yana mai cewa iyalan da suka rasa matsugunansu na matukar bukatar tallafin jin kai.

Ya zuwa karfe 3:00 na ranar Laraba, mazauna yankin sun ce wasu daga cikinsu ba su ci abinci ko sau guda ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM