Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Umar Abubakar-Tafida, ya yi watsi da ikirarin cewa cire shi daga matsayin abokin takarar Gwamna Nasir Idris a zaben gwamna na 2027 yana da alaka da hukuncin Kotun Koli kan zaben 2023.
Jam’iyyar APC ta sanar a ranar 16 ga Agusta cewa an maye gurbin Abubakar-Tafida da tsohon Kwamishinan Kudi, Alhaji Ibrahim Muhammad-Augie, a matsayin abokin takarar Gwamna Idris a zaben gwamna na 2027.
Jam’iyyar ta ce an dauki matakin ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki da kwararru kan harkokin shari’a game da karar da ta shafi zaben gwamna na 2023 da Abubakar-Tafida.
Da yake magana a ranar Laraba, lokacin da magoya bayansa, abokan siyasa da masu yi masa fatan alheri suka ziyarci gidansa da ke Argungu, Abubakar-Tafida ya bayyana ikirarin da ke alakanta cire shi da hukuncin Kotun Koli a matsayin yunkurin abokan hamayyarsa na siyasa na amfani da shari’ar da ta shafi zaben gwamna na 2023 wajen bata masa suna.