Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare ranar Laraba, kwanaki shida kacal bayan hatsarin kwale-kwale da ya afku a yankin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 65.
Maharan sun kuma harbe wasu mazauna ƙauyen guda bakwai, inda suka jikkata kuma a halin yanzu suke karɓar magani a asibiti.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun kai farmaki ne musamman kan iyalan da suka kasance cikin waɗanda za su amfana da tallafin naira miliyan ɗaya da Gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar za ta bai wa kowane iyali na waɗanda suka rasa ’yan uwansu a hatsarin kwale-kwalen.
Da yake tabbatar da harin, shugaban ƙauyen Gorau, Alhaji Aliyu Magaji Na-Batsami, ya ce maharan sun rika shiga gida-gida ne suna neman kuɗin tallafin.
Ya ce maharan sun kutsa kusan kowane ɗaki a gidansa, suna tambayar inda aka ajiye naira miliyan ɗaya da aka bai wa iyalan waɗanda hatsarin ya shafa.
A cewar sarkin, mutanen huɗun da aka kashe a harin su ne Bashar Sani, Ila Malam Makeri, Isa Ibrahim da Ali Aminu.
Ya ce adadin waɗanda suka mutu ko suka jikkata zai iya ƙaruwa in ba don ɗaukin gaggawa da jami’an tsaro suka kai masu ba.