Mukaddashin kakakin rundunar, Kanal Olaniyi Osoba, ya ce sojojin sun samu sahihin bayanan sirri kan shirin musayar kuɗin fansar da aka shirya yi domin sakin matar da aka sace a gonarta a watan da ya gabata.
Ya ce bayan samun bayanan, sojojin sun gaggauta tura dakarunsu domin dakile musayar kuɗin fansar.
A cewar Osoba, yayin da ’yan ta’addan suka hango sojojin suna matsowa, sun yi ƙoƙarin tunkarar su da harbi, amma dakarun suka yi galaba a kansu da ƙarfin makamansu.
Kakakin ya ce hakan ya tilasta wa ’yan bindigar janyewa cikin rudani, inda suka bar matar da suka yi garkuwa da ita a wurin.
Daga bisani, sojojin sun samu nasarar kuɓutar da matar, wadda aka same ta cikin ƙoshin lafiya ba tare da wani rauni ba.
Ya ƙara da cewa an kai matar lafiya sannan aka haɗa ta da iyalanta a ƙaramar hukumar Danko-Wasagu ta jihar Kebbi.
Bayan ceto matar, sojojin sun gudanar da bincike da sintiri a hanyar da ’yan ta’addan suka bi yayin tserewa, domin tabbatar da cewa an tsabtace yankin kuma babu sauran barazana kafin dakarun su koma sansaninsu.
A wani samame na daban, sojojin sun gudanar da sintirin share fage da tabbatar da iko da yankin a ƙaramar hukumar Ngaski ta jihar Kebbi.
Rundunar ta ce an kammala sintirin cikin nasara ba tare da wani mummunan lamari ba, lamarin da ta ce ya ƙara tabbatar da tsaron yankin daga ayyukan miyagun laifuka.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da gudanar da ayyukan leƙen asiri, sintiri da samame domin dakile ayyukan ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka a yankin.