Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi ya ce adawar siyasa ce ke ƙara rura wutar rashin tsaro a Arewa
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya yi gargadin cewa bambance-bambancen siyasa tsakanin shugabannin yankin Arewa ta Tsakiya na samar da damar da mayaƙa da sauran masu aikata laifuka ke amfani da ita wajen cin gajiyar matsalolin tsaro da yankin ke fuskanta.
Sule, wanda ya yi wannan magana a yayin taron koli na tsaro a shiyyar Arewa ta Tsakiya da aka gudanar a gidan gwamnatin Jihar Benue da ke Makurdi, ya yi kira ga shugabannin siyasa a faɗin yankin da su cire siyasa daga batutuwan tsaro, tare da gina amana da hanyoyin musayar bayanan sirri domin tunkarar matsalar rashin tsaro.
Rahotanni sun ce Ma’aikatar Tsaro ce ta shirya taron, tare da haɗin gwiwar Ofishin Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Hulɗa da jama’a.