Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta kori ma’aikata sama da 40 cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata saboda zargin cin hanci da almundahana.
Da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja, shugaban na EFCC ya ce an gurfanar da fiye da biyar daga cikinsu yanzu haka a su a kotu, yayin da ake shirin fara shari’ar wasu.
Olukoyede ya ce hukumar ta kuma dawo da kusan Naira tiriliyan1.23 dala miliyan 684.48, da fam na England dubu 373,905 da kuma euro 9.34m tsakanin Oktoba 2023 da Yuni 2026.
Ya jaddada cewa ma’aikatan EFCC ba za su iya yaki da cin hanci yadda ya kamata ba yayin da su kansu ke aikata irin wannan laifi.
Shugaban ya ƙara da cewa hukumar za ta ƙarfafa riƙon amana tsakanin ma’aikatan ta ta hanyar bunƙasa walwalar su da kuma ɓullo da wasu shirye-shirye da zai nada dama a riƙa basu kyatuttuka.