NE

News Elementor

Sojoji sunyi nasarar ceto mutane 4 da akayi garkuwa da su a jahohin Katsina da Nasarawa

Rundunar Sojojin Sector 2 na rundunar haɗin gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA tare da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa sun ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su a wasu ayyukan tsaro daban-daban a jihohin Katsina da Nasarawa.

A Jihar Katsina, sojoji sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su yayin wani samame da suka gudanar a kan hanyar Dandume zuwa Sheme, a ƙaramar hukumar Dandume.

An ce an ceto mutanen ne ranar Alhamis, bayan da mazauna yankin suka aika da kiran gaggawa ga jami’an tsaro, suna sanar da su ayyukan wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne a kan hanyar.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin gwiwar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce bayan samun rahoton, sojoji tare da ’yan sanda sun gaggauta kai ɗauki zuwa yankin.

Ya ce jami’an tsaron sun yi arangama da ’yan ta’addan, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa cikin daji. A cewarsa, ’yan ta’addan sun bar waɗanda suka yi garkuwa da su a yayin ƙoƙarin tserewa daga jami’an tsaron.

Danja ya ce bayan binciken yankin, an samu nasarar ceto mutane ukun tare da kwato motoci biyu da ake zargin ’yan ta’addan ne suka yi amfani da su.

Ya ƙara da cewa an miƙa mutanen da aka ceto da motocin da aka kwato ga jami’in ’yan sanda na sashen Dandume domin ɗaukar matakan da suka dace.

A Nasarawa kuma, rundunar ’yan sandan jihar ta ce ta samu wata gagarumar nasara, inda ta ceto wata mata da aka yi garkuwa da ita tare da kama mutane 11 da ake zargi da fashi da makami a wasu ayyuka daban-daban.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Ramhan Nansel, ya ce wata mai suna Favour Innocent daga ƙauyen Ajyga, wadda aka yi garkuwa da ita daga gidanta ranar 3 ga Agusta da misalin ƙarfe 9 na dare, an ceto ta washegari a yankin dajin Nunku da ke ƙaramar hukumar Akwanga.

Ya ce haɗin gwiwar ’yan sanda, mafarautan gida da matasan yankin ne ya taimaka wajen ceto matar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM