NE

News Elementor

Yadda aka yi jana’izar Marigayi Sarkin Gumel Ahmad Muhammad Sani cikin alhini da juyayi

Dubban al’ummar jihar Jigawa da sauran sassan Najeriya, sarakunan gargajiya, ’yan siyasa da sauran manyan baki sun halarci sallar jana’izar marigayi Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Muhammad Sani II, wanda ya rasu yana da shekaru 85.

An gudanar da sallar jana’izar ne a fadar marigayi sarkin da ke Gumel da yammacin Juma’a, 4 ga Satumba 2026, bayan rasuwarsa a birnin Alkahira na ƙasar Masar a ranar Alhamis, 3 ga Satumba, sakamakon rashin lafiya.

Marigayi Sarkin Gumel, wanda aka haife shi a shekarar 1942, ya shafe shekaru masu yawa yana jagorantar masarautar Gumel tare da kula da al’adunta, tarihinta da dabi’un al’ummarta.

Daga cikin manyan mutanen da suka halarci jana’izar akwai Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya jagoranci tawagar fadar shugaban ƙasa, da Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi.

Haka kuma, gwamnonin Kano da wasu jihohin Arewa, manyan ’yan siyasa, jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya, ciki har da sarakunan Kano, Jigawa da sauran masarautu, sun halarci jana’izar domin yi wa marigayin bankwana.

Rahotanni sun bayyana cewa garin Gumel ya cika da makoki, yayin da mazauna garin da baƙi daga wurare daban-daban suka taru domin yin bankwana da marigayi sarkin.

Marigayin ya bar ’ya’ya kusan 33, maza 21 da mata 12, baya ga jikoki da dama.

Da yake jawabi a wajen jana’izar, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya roƙi Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya ba shi rahama da hutawa, tare da saka masa da alherin ayyukan da ya yi.

Shettima ya kuma roƙi Allah Ya bai wa iyalan marigayin, al’ummar Masarautar Gumel da gwamnatin da jama’ar jihar Jigawa haƙurin jure wannan babban rashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM