Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa ya ce girman dajin Sambisa yana yi wa jami’an tsaro wahalar shiga, lamarin da ke ƙara wahalar da aikin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Musa ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today, inda ya kare matakan da gwamnati ke ɗauka wajen yaƙi da ta’addanci da garkuwa da mutane a ƙasar nan.
Ministan ya ce jami’an tsaro sun ci gaba da ceto ’yan Najeriya da aka yi garkuwa da su, amma ’yan ta’adda kan tsere zuwa manyan dazuzzuka kafin sojoji su iya gano inda suke.
Ya ce dajin Sambisa wani abu ne da ’yan Najeriya ke raina girmansa, yana mai cewa girmansa ya yi daidai da na ƙasar Belgium.
A cewar Musa, ’yan ta’adda suna amfani da faɗin dajin wajen ɓoyewa jami’an tsaro bayan sun kai hare-haren sace mutane.
Ya ce ƙungiyoyin na iya shiga cikin dazuzzukan kafin labarin harin ya isa ga jami’an tsaro, lamarin da ke sa ya yi wahala sojoji su gano inda suke cikin gaggawa.