Mai fafutuka a kafafen sada zumunta, Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, ya nemi afuwar sojoji, ’yan sanda, jami’an kwastam da na shige da fice bisa kalaman da ya yi wadanda suka tada kura a taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyi ta nkasa karo 66.
Otse, a cikin wani bidiyo da ya wallafa, ya ce ya sake nazarin jawabin nasa kuma ya fahimci cewa ya yi wa jami’an tsaro waɗanda ke sadaukar da rayukansu wajen kare ’yan Najeriya rashin adalci.
A lokacin da yake magana a taron da aka gudanar a Port Harcourt, Jihar Rivers, Otse ya kira jami’an soja, ’yan sanda, shige da fice da kwastam da sunan jami’an tsaron da ba a san da sub a, yayin da yake magana kan matsalar rashin tsaro.
Sai dai a cikin bidiyon da ya fitar a njiya Juma’a, Otse ya ce kalamansa ba wai yana nufin zargin dukkan jami’an tsaro da hannu a ayyukan laifi ba ne.
Ya ce abin da ya fi damunsa shi ne sojojin da ke yaƙi da Boko Haram da sauran barazanar tsaro a cikin dazuzzuka.