NE

News Elementor

‘Yan bingida sun hallaka mutum 10, tare da yin garkuwa da mutane 38 a ƙaramar hukumar Rabah ta jihar Sokoto

Akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari a Tofa, ƙaramar hukumar Rabah ta jihar Sokoto.

An ce harin ya faru ne a daren Lahadi, inda maharan suka shiga al’ummar, suka rika harbin mazauna sannan suka yi garkuwa da mutane da dama.

Majiyoyin yankin sun shaida wa Punch cewa adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ya kai tsakanin 38 zuwa 40, sai dai har yanzu ana ci gaba da tantance ainihin adadin.

’Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da dabbobi masu yawa na mazauna yankin tare da kwashe wasu kayayyaki a lokacin harin.

Lamarin ya ƙara jefa al’ummar Rabah cikin fargaba, musamman kan yadda maharan suka samu damar shiga Tofa, suka shafe lokaci suna kai hari, kashe mutane da yin garkuwa da wasu ba tare da jami’an tsaro sun dakile su ba.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufai, ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce rundunar za ta fitar da cikakkun bayanai bayan kammala tattara rahotonta.

Jaridar Punch ta ce ba a tabbatar da ainihin adadin waɗanda aka kashe da waɗanda aka yi garkuwa da su ba a lokacin da aka wallafa wannan rahoton.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM