’Yan ta’adda sun kashe mutane 12 tare da jikkata wasu biyu a kauyen Nzangula da ke ƙaramar hukumar Gombi ta jihar Adamawa.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa The PUNCH cewa mambobin Boko Haram sun mamaye kauyen da sanyin safiyar Litinin, inda suka rika harbin mazauna tare da kona gidaje.
Ya ce kawo yanzu an gano gawarwaki 11, yayin da ake ci gaba da neman ɗaruruwan mutanen da har yanzu ba a san inda suke ba. Tawagar masu aikin ceto da jami’an tsaro na gudanar da bincike a cikin dazuzzukan yankin.
Wani mazaunin yankin ya kuma bayyana cewa matarsa da wasu ’yan uwansa biyu na daga cikin waɗanda aka kashe a harin.
Shugaban ƙaramar hukumar Gombi, Markus Ishaya, ya tabbatar da harin, inda ya ce mutane 12 ne aka kashe, yayin da wasu biyu suka jikkata kuma suke karɓar magani a Asibitin Cottage da ke Gombi.
Ya ƙara da cewa an yi garkuwa da wata mata guda, yayin da aka ƙona cocin EYN da wasu gidaje uku, sannan aka lalata shaguna biyu.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, bai amsa kiran waya ko saƙonnin da aka tura masa domin tabbatar da lamarin ba.