NE

News Elementor

Ƙungiyar Ibo ta Arewa ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu tare da yi masa alƙawarin kuri’u miliyan biyu a zaɓen 2027

Ƙungiyar siyasa ta Igbo Delegates Assembly mai wakiltar al’ummar Ibo a jihohin Arewa 19 da Abuja, ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ƙungiyar ta kuma yi alkawarin tattara ƙuri’u miliyan biyu domin jam’iyyar APC a zaɓen 2027, tare da bayyana cewa za ta goyi bayan ‘yan takarar APC na gwamna da na majalisun dokoki a jihohin Arewa da Abuja.

Daraktan Janar na Igbo Political Movement ƙarƙashin ƙungiyar, Chief John Amaechi Onwe, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna ranar Asabar.

Onwe ya ce matakin bai dogara da ƙabilanci ba, duk da cewa tsohon Gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027, Peter Obi, ɗan asalin Ibo ne.

Ya ce ƙungiyar ta yanke shawarar ne bayan tuntubar ’yan kasuwa, masana’antu, matasa, mata da shugabannin al’umma a jihohin Arewa 19 da Abuja, tare da nazarin ayyukan gwamnatin Tinubu cikin shekaru uku da suka gabata.
Ƙungiyar, wadda ta yi amfani da taken “Ci gaba, Wadata da Haɗin kai”, ta ce sauya tsarin tallafin man fetur da haɗa kasuwannin canjin kuɗin waje na daga cikin matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka waɗanda suke da wahala a farko amma suke da muhimmanci.

Ta kuma yaba wa ayyukan raya ababen more rayuwa da gwamnatin ta ke gudanarwa, ciki har da Lagos-Calabar Coastal Highway, Enugu-Port Harcourt Expressway da hanyoyin shiga gadar Second Niger Bridge.

Onwe ya ce waɗannan ayyukan za su taimaka wa ’yan kasuwar Ibo wajen jigilar kayayyaki da bunƙasa harkokin kasuwanci. Ya kuma yi ikirarin cewa dubban ’yan kasuwar Ibo a manyan cibiyoyin kasuwanci na Arewa sun samu tallafin kuɗi ba tare da shiga tsakani na ‘yan siyasa ba.

Ƙungiyar ta kuma yaba wa shirye-shiryen gwamnatin tarayya na kudin rancen ɗalibai, tallafa wa masana’antu da bunƙasa harkar gas, da kuma ƙoƙarin sauƙaƙa gudanar da kasuwanci.

Ta kuma yabawa ƙarin alawus ɗin NYSC daga N33,000 zuwa N77,000, tana mai cewa hakan na nuna kulawa da jin daɗin matasa.

Ƙungiyar ta ce za ta tura tsarinta zuwa matakin ƙasa domin wayar da kan mambobinta game da manufofin gwamnatin Tinubu da kuma tattara goyon baya ga APC a zaɓen 2027.

Ta kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su yi watsi da wariyar ƙabilanci, rarrabuwar kai da siyasar ƙiyayya, tana mai cewa Najeriya na buƙatar ci gaba da manufofin da ake aiwatarwa, ba rushe su ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM