Taron wanda aka gudanar a gidan Sanata Abdul’aziz Abubakar Yari a Talata Mafara dake jihar Zamfara.
Kafar yada labarai ta Legit ta rawaito ceqa malaman sun fito ne daga Bakura da Talata Mafara, kuma taron addu’ar ya shafi neman zaman lafiya da kuma yi wa Shugaba Bola Tinubu da APC fatan nasara a zaben 2027.
Daga cikin makaman akwai Imam Yahuza, Magawata Abdullahi, Malam Shehu Dakko, Imam Bala Fagon da kuma Na’ibi Tasi’u na Tungar Nagudai.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safe ranar Asabar, 12 ga Satumba, a kan hanyar Dakko zuwa Damri da ke Ƙaramar Hukumar Bakura.
TRT Afrika Hausa ta rawaito cewa, ’yan sandan Zamfara sun ce ’yan bindiga ɗauke da makamai sun yi wa motar malaman kwanton ɓauna, kafin su yi garkuwa da su yayin da suke kan hanyarsu ta komawa gida.
Bayan samun rahoton, jami’an tsaro sun fara bincike a yankin, ciki har da dazuzzukan da ke kewaye da hanyar, domin gano malaman da kuma kama waɗanda suka yi garkuwa da su.
Kwamishinan ’yan sandan Zamfara, CP A. M. Bello, ya umarci jami’an da su ƙara kaimi wajen aikin ceto, tare da tabbatar da dawowar malaman cikin aminci.