NE

News Elementor

Rundunar ‘ƴan sanda ta yi gargadi game da yiwuwar kai hare-hare a makarantu da wuraren ibada

Rundunar yansandan Nigeria ta yi gargadi game da shirin kai hare-hare kan makarantu, cibiyoyin horas da NYSC, wuraren ibada da sauran muhimman cibiyoyi a fadin kasar nan.

A wata takardar tsaro da ta aikewa dukkan rassanta a fadin Nigeria, rundunar ta ce bayanan sirri daga sashen ayyuka na musamman sun tabbatar da cewa, yan ta’adda na yin wani shiri domin kaddamar da hare-hare a wuraren da aka ambata.

An aike da sakon ne ga mataimakan babban sifeton yansanda masu kula da shiyyoyi 17, da rundunonin yansandan kota-kwana, da masu yaki da ta’addanci da sauran jami’ai na musamman, kazalika da kwamishonin yansanda na dukkan jihohi.

A cewar rundunar, bayanan sirri sun gano yadda yan bindiga ke kai komo daga Katsina zuwa Kaduna har zuwa Plateau.

Sashen ayyuka na rundunar ya kuma umarci dukkan jami’an hukumar su tsaurara matakan tsaro kan iyakokin jihohi, da wuraren shige da fice da sauran cibiyoyi domin dakile kwararar yan bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM