NE

News Elementor

Gwamnatin jihar Kebbi ta musanta kashe Naira Biliyan 21.5 wajen siyawa mutane kujerun Hajji

Gwamnatin jihar Kebbi ta musanta kashe Naira Biliyan 21.5 wajen siyawa mutane kujerun Hajji Gwamnatin jihar Kebbi ta ƙaryata rahoton da ya ce ta sayi kujerun Hajji har na Naira biliyan 21.5 domin taɓawa ga ƴan jihar.

Hajj Reporters ta rawaito cewa wani mai suna Evangelist Ibrahim Dikko ne ya yi zargin cewa gwamnatin jihar ta kashe waɗannan maƙudan kuɗaɗe don rabawa mutane kujerun aikin Hajji.

A wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan jihar, Ahmed Idris ta fitar, gwamnatin ta ce sam wannan rahoto ƙarya ne domin kuɗin da ake magana akai, na kujeru ne da maniyyata su ka biya.

“An ja hankalinmu kan wani labari da Evangelist Ibrahim Dikko ya wallafa, inda ya yi zargin cewa Gwamnatin Jihar Kebbi ta ware sama da Naira biliyan 21.5 domin daukar nauyin alhazan jihar zuwa Ƙasa Mai Tsarki.”

Kuɗaɗen da aka ambata a cikin labarin, kuɗaɗe ne da kowane maniyyaci zuwa aikin ya biya domin biyan kujerar Hajji.”Naira biliyan 21.5 da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi ta tura, na wakiltar kuɗaɗen da sama da maniyyata 3,000 da ke shirin zuwa aikin Hajjin 2027 suka biya,” in ji Idris.

Ya kara da cewa hukumar na aiki ne a matsayin hanyar da ake bi wajen karɓa, sarrafawa da kuma tura kuɗaɗen da maniyyata su ka biya zuwa Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta Najeriya (NAHCON).

Ya ƙara da cewa ba a yi amfani da kuɗaɗen gwamnati ko wani kaso daga cikin kasafin kuɗin jihar wajen biyan waɗannan kuɗaɗen Hajji na kowane mutum ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM