Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayar da umarnin dakatar da Kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence na Jihar Neja, Suberu Aniviye, nan take, biyo bayan mutuwar wasu da ake zargin masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne a jihar.
Ministan ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin, wanda rahotanni suka ce ya faru ne a yankin M.I. Wushishi/Lukoto da ke Minna, babban birnin jihar, da sanyin safiyar Alhamis.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa ministan shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Alao Babatunde, ya fitar a ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, an kama mutanen da ake zargin masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne a yayin samamen tabbatar da doka da aka gudanar a wasu sassan Jihar Neja a ranakun 15 da 16 ga Satumba, 2026.