NE

News Elementor

An sanya dokar hana fita a birnin Minna na Jihar Neja

Hukumomi a jihar Neja sun ƙaƙaba dokar hana fita a Minna, babban birnin jihar Neja sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke.

Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan yaɗa labarai, Zayyanu A Salihu ya wallafa sanarwar a shafinsa na Instagram.

Ya ce dokar ta tsawon sa’a 24 za ta soma aiki bayan sallar Juma’a.Hukumomi sun shawarci jama’a da su mutunta dokar.

Wani mazaunin Unguwar Tunga Sabon Titi inda lamarin ya faru, wanda kuma ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa matasan da suka fusata sun yi ta jefe-jefe yayin da ƴansanda kuma ke harbi.

A cewarsa, ƴansanda sun harbi mutum huɗu kuma a cikinsu mutum guda ya mutu nan take.Da farko, jami’ai sun yi zargin cewa wata cuta ce ta yi sanadin mutuwar matasa da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Tuni dai gwamnatin jihar ta Neja ta sanar da kafa kwamitin bincike don gano musabbabin mutuwar matasanLamarin ya sa gwamna Mohammed Umar Bago ayyana makokin kwanaki uku tare da dakatar da yaƙin neman zaɓensa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan kallon masu sukar ta a matsayin makiya

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta daina kallon duk masu sukar manufofinta a matsayin makiyan Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta rika karɓar suka mai ma’ana. Sanusi ya bayyana haka ne yayin wani taron shugabanci na Oxford Global Think Tank Leadership Conference da aka...

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM