NE

News Elementor

Tinubu ya tsawaita hutun da yake yi a ƙasashen Turai

Fadar shugaban kasa ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsawaita hutun aikinsa da wasu kwanaki, kuma ana sa ran zai dawo Najeriya a ƙarshen mako.

Tinubu ya bar Najeriya zuwa London a ranar 30 ga Agusta domin fara hutun aiki, daga bisani ya zarce Paris, Faransa, inda ya gana da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, da ɗan kasuwa Vincent Bolloré.

Fadar Shugaban Ƙasar ta ce duk da kasancewarsa hutu, Tinubu na ci gaba da bibiyar harkokin gwamnati da bayar da umarni kan wasu muhimman batutuwa.

Ta ce daga cikin matakan da ya ɗauka akwai kafa kwamitin bincike mai zaman kansa kan mutuwar masu hakar ma’adinai 37 a Minna bayan da aka tsare su.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilci Tinubu a wasu taruka, ciki har da Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da ake gudanarwa a New York.

Sai dai Fadar Shugaban Ƙasar ta ce Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, zai ci gaba da wakiltar Tinubu a wasu ayyukan gwamnati.

A fannin siyasa kuwa, Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa, Sanata Abubakar Yari, na jagorantar tattaunawa da wasu manyan sarakunan gargajiya a ƙasar.

Fadar Shugaban kasar ta kuma soki ikirarin da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da wata kungiyar masu fafutukar siyasa da ke Amurka suka yi kan rashin halartar Tinubu taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Mai ba Shugaban kasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya fitar da sanarwar a ranar 21 ga Satumba 2026.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM