Sakataren yada labaran jamiyyar na kasa, Bolaji Abdullahi ne ya bayyana hakan yayin wata hira a shirin siyasa na gidan television din Channels.
A cewarsa, yanzu haka jamiyyar ta fara shirye-shirye domin ganin yadda za ta tattara kuri’unta da kanta, yana mai gargadin cewa, ba za su amince da rashin tabbas na hukumar INEC ba.
Ya buga misali da zaben 2023 lokacin da ya yi takarar Sanata, inda ya ce yan takara da dama sun amince da INEC lokacin da ta sheda musu cewa za ta tura sakamakon zabe kai tsaye ta na’ura.
To sai dai, Abdullahi ya koka kan cewa, ba a tura sakamakon ta na’ura ba saboda abin da hukumar ta kira tangardar na’ura, inda ya ce an sha su sun warke, kuma a yanzu ba za su yarda a maimaita musu irin hakan ba.