Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce ta karɓi allurar rigakafin cutar Diphtheria, inda za a fara yi wa yara rigakafin a jihar daga ranar Alhamis.
Kwamishiniyar Lafiya ta jihar, Dr Nafisa Maradun ce ta bayyana hakan a Gusau ranar Talata.
Wannan mataki ya biyo bayan barkewar cutar Diphtheria a jihar, wacce ta hallaka mutane 44 daga cikin mutane 367 da aka tabbatar sun kamu da cutar, yayin da sama da 200 suka samu sauƙi.
Kwamishiniyar ta ce an samu rahoton masu ɗauke da cutar a kananan hukumomi 11 na jihar, sannan za a fara rabon allurar rigakafin ga yara a yankunan da abin ya shafa daga Alhamis.
Ta ce binciken ma’aikatar lafiyar jihar ya nuna cewa yawancin yaran da suka kamu da cutar ba su samu rigakafin ba, ko kuma ba su kammala allurar rigakafin da ake yi wa yara a kai a kai ba.