Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya ce zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai kasance fafatawa tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da talakawan Najeriya, maimakon tsakanin jam’iyyun siyasa.
Makinde ya bayyana hakan ne ranar Talata a Katsina, yayin wani taron jama’a na Arewa maso Yamma da tawagar yaƙin neman zaɓensa ta shirya domin gabatar da shirin jam’iyyar mai suna “Reset Nigeria”.
Ya ce: “Ba APC da APM ba ne za su fafata, ko APM da APC, ko APC da ADC; APC da ’yan Najeriya ne za su fafata.”
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su mallaki katin zaɓensu (PVC) tare da taka rawa sosai a zaɓe. Ya ce shirin “Reset Nigeria” ya mayar da hankali kan tattalin arziki, ilimi, rashin tsaro da gyaran hukumomi.
Makinde ya kuma musanta ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Jihar Oyo naira biliyan 50 domin inganta filin jirgin saman Ibadan, yana mai cewa gwamnatin jihar ce ke ɗaukar kashi 100 cikin 100 na kuɗin aikin.
Ya kuma nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a ƙasar, inda ya ambaci kisan matasa 37 a Jihar Neja.