Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya dawo Najeriya daga ƙasar Amurka a ranar Lahadi domin ci gaba da yakin neman zaɓensa na shugaban ƙasa a 2027.
Mista Sowore ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Lahadi.
Ya ce yana matuƙar farin ciki da komawarsa wajen iyalansa da kuma ƙasarsa, bayan kammala tafiyarsa zuwa Amurka.
A cewarsa, ya tafi Amurka ne sakamakon abin da ya bayyana a matsayin kamawa, tsarewa, takaita masa zirga-zirga da kuma ƙwace fasfo ɗinsa na ƙasa da ƙasa da hukumomin tsaron Najeriya suka yi.
Mista Sowore ya ce a lokacin da yake Amurka, ya gana da ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje, magoya bayansa, masu fafutuka da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna halin da ƙasar ke ciki da kuma manufofinsa na siyasa.
Ya kuma ce ya halarci wata zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa a birnin New York, tare da ci gaba da fafutukar ganin an bai wa ’yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje damar kada kuri’a.