Rahotanni sun ce akalla mutane 18 ne wani kare da ake zargin ya kamu da cutar hauka ya ciza a ƙaramar hukumar Garko ta jihar Kano.
Bayan faruwar lamarin, Hukumar Tsaron Gandun Daji ta Najeriya (NFSS), reshen Garko, ta ƙaddamar da wani aikin neman karen da wasu karnuka biyu da ake zargin su ma sun kamu da cutar.
Kwamandan Hukumar NFSS a jihar Kano, a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, CSF Usman Abdullahi Umar, ya sanya wa hannu, ya ce lamarin ya biyo bayan wani rahoton neman agaji da ofishin hukumar da ke Garko ya samu.
A cewar sanarwar, karen ya fara kai hari tare da cizon mutane 11 a garin Garko, kafin daga bisani ya nufi wasu ƙauyuka da ke makwabtaka da garin.
Sanarwar ta ce daga bisani wasu mutane bakwai ne aka kuma ciza a garuruwan Raba, Kadage, Gurjiya da Dausai, lamarin da ya sa adadin mutanen da aka ruwaito an ciza ya kai 18.