Sabbin bayanai sun bayyana game da kama fitaccen ɗan siyasar Jihar Yobe, Wakil Goni Mama, wanda aka fi sani da Mai Salati, da zargin bayar da tallafin kayan aiki da sauran buƙatu ga ƙungiyoyin ta’addanci na Boko Haram da ISWAP da ke aiki a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa sojojin Operation HADIN KAI ne suka kama ɗan siyasar a ranar Asabar, bayan samun bayanan sirri da suka danganta shi da mutanen da ake zargin suna taimaka wa ’yan ta’adda.
Lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma, inda wasu ke zargin akwai siyasa a cikin batun.
Sai dai wasu majiyoyi masu masaniya kan aikin sojin, waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu, sun shaida wa jaridar cewa an kama Mai Salati ne bisa zargin taimaka wa ’yan ƙungiyoyin ISWAP da Boko Haram da kayayyaki da sauran buƙatu.
Majiyoyin sun bayyana cewa kama shi ya biyo bayan zargin yunƙurinsa na ba jami’an soji cin hanci domin a saki wasu waɗanda aka kama a Kanamma, Jihar Yobe.
A cewarsu, kamen ya biyo bayan binciken sirri da kwamandan Sector 2 da rundunar 27 Task Force Brigade suka gudanar domin gano tare da cafke ɗan siyasar, wanda ake zargin yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da kayayyaki ga ’yan ta’adda.
Sun ce a lokacin da ake shirya miƙa waɗanda aka kama a Kanamma domin ci gaba da bincike, Mai Salati ya yi yunƙurin shiga tsakani domin a sake su, ta hanyar bayar da kuɗi ga sojoji.
Sai dai rahoton ya ce jami’an sojin sun ƙi karɓar kuɗin, suka kama shi tare da fara shirye-shiryen miƙa shi Maiduguri domin zurfafa bincike da yiwuwar ɗaukar matakin shari’a.
Haka kuma, wani faifan bidiyo da DAILY NIGERIAN ta gani, ya nuna ɗan siyasar yana ƙoƙarin miƙa kuɗi ga jami’an soji dangane da yunƙurin sakin waɗanda aka kama.
A wani ɓangare kuma, ƙungiyar Yobe Network Against Violent Extremism ta yi kira ga al’umma da ’yan siyasa da su bai wa hukumomin tsaro damar kammala bincikensu kan lamarin Mai Salati.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa yaɗa jita-jita a kafafen sada zumunta da bayyana batun ta fuskar siyasa na iya karkatar da hankalin hukumomin tsaro daga aikinsu.
A cikin wata sanarwa da jagoran ƙungiyar, Ibrahim Goni, ya fitar, ya bayyana cewa yankin Arewa maso Gabas ya sha wahala sosai sakamakon hare-haren ta’addanci, waɗanda suka jawo raba dubban iyalai da muhallansu tare da asarar rayukan jami’an tsaro.
Ya ce duk wani sahihin zargi da ya shafi samar da kuɗi, kayayyaki, ɗaukar ma’aikata, ɓoye ’yan ta’adda ko taimaka musu ta kowace hanya, ya kamata a gudanar da cikakken bincike a kansa, ba tare da la’akari da matsayin siyasa ko zamantakewar wanda ake zargi ba.