Ƙungiyar masu buƙata ta musamman daga jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja ta yi alkawarin tattara kuri’u miliyan biyar domin zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Shugaban ƙungiyar ta Society for Persons with Disabilities Forum, Comrade Yarima Sulaiman Ibrahim, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron wayar da kan masu buƙata ta musamman kan muhimmancin shiga zaɓe, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin Kano.
Yarima ya ce ƙungiyar na goyon bayan Tinubu da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, domin su sake komawa kan mulki, saboda abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarinsu na inganta walwalar masu buƙata ta musamman da kuma ba su damar shiga harkokin siyasa.
Ya bayyana kafa Hukumar Kula da Masu Buƙata Ta Musamman ta Ƙasa da kuma naɗa mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokinsu a matsayin wasu daga cikin matakan da suka yaba.
Sai dai ya bukaci gwamnatin tarayya ta aiwatar da tanadin kashi biyar cikin ɗari na wakilcin masu buƙata ta musamman a muƙaman gwamnati, ciki har da ministoci da shugabannin hukumomi.
A cewarsa, ƙungiyar ta kuma cimma matsaya da Gwamna Abba Kabir Yusuf cewa za a ba masu buƙata ta musamman muƙamin kwamishina idan ya sake lashe zaɓen gwamna a 2027.
Yarima ya ce masu buƙata ta musamman a Arewacin Najeriya sun kai kusan miliyan biyar, kuma tuni suka fara wayar da kan mambobinsu da iyalansu domin cimma wannan buri, yana mai cewa adadin kuri’un da za su tattara na iya haura miliyan biyar.
A nata jawabin, Kwamishiniyar Harkokin Mata, Yara da Masu Buƙata Ta Musamman ta Kano, Amina HOD, ta ce gwamnatin jihar na ƙoƙarin inganta rayuwar masu buƙata ta musamman ta fuskar ilimi, lafiya, aikin yi da shiga harkokin al’umma.
Ta bayyana cewa gwamnati na rarraba kujerun guragu ga masu matsalar laka, tallafa wa wasannin nakasassu da kuma shirin kafa hukumar musamman domin kula da bukatunsu.
Ta kuma ce ana gudanar da shirin koyar da matasa masu buƙata ta musamman dabarun fasahar zamani tare da haɗin gwiwar hukumar raya ƙasashen Jamus, GIZ, domin taimaka musu samun ƙwarewar da za ta buɗe musu damar aiki.
An gudanar da taron ne domin wayar da kan masu buƙata ta musamman kan muhimmancin kaɗa ƙuri’a da kuma jawo hankalin hukumomi kan matsalolin da ke hana su cikakken shiga harkokin zaɓe.