NE

News Elementor

Tinubu ya umarce shugabannin hukumomin tsaro su rusa dukkan sansanonin ’yan bindiga tare da ceto mutanen da aka sace a Nigeria

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gana da shugabannin hukumomin tsaro na ƙasar nan, inda ya umarce su da su rusa dukkan sansanonin ’yan bindiga tare da ceto mutanen da aka sace.

Ganawar, wadda ta ɗauki tsawon sa’o’i, ta kuma mayar da hankali kan yadda za a samar da yanayin da zai ba da damar gudanar da babban zaɓen shekarar 2027 cikin lumana.

Da yake magana da manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan taron, Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya ce sun je fadar shugaban ƙasa ne domin yi wa shugaban ƙasa bayani kan halin da tsaro yake ciki a ƙasar nan, inda ya ƙara da cewa yayin da zaɓe ke ƙaratowa, yana da muhimmanci a sanar da shugaban ƙasa abubuwan da ke faruwa.

Musa ya ce dukkan shugabannin hukumomin tsaro sun halarci taron, kuma Shugaba Tinubu ya umarce su da su tashi tsaye, su gano tare da ceto duk mutanen da aka sace ko aka yi garkuwa da su, a duk inda suke.

Ministan ya ce sun tattauna sosai kan lamarin, kuma Shugaban Ƙasa ya bayyana karara cewa yana son a gudanar da zaɓe cikin ’yanci, adalci da gaskiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM