Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana dalilin da ya sa yake son tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027, tare da mara wa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasar jam’iyyar, baya.
Kwankwaso ya ce kiransa ya samo asali ne daga tsohuwar alaƙar siyasa da ke tsakaninsa da Atiku, da kuma buƙatar samar da sabon tsarin siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya tabbatar da cewa yana son Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya janye daga takarar.
Da aka tambaye shi ko yana nan daram kan matsayarsa ta cewa ya kamata Atiku ya yi watsi da burinsa na zama shugaban ƙasa, tsohon gwamnan Jihar Kano ya amsa da cewa “eh.”
Kwankwaso ya bayyana cewa a kwanan nan ya yi amfani da ziyarar da wasu Fulani daga sassa daban-daban na ƙasar suka kai masa domin ƙarfafa musu gwiwar su tattauna da Atiku game da janyewarsa daga takarar.
Ya jaddada cewa matsayarsa ba ya da alaƙa da wata ƙiyayya ta kansa, yana mai cewa ya san Atiku tsawon shekaru da dama kuma sun yi aiki tare a ayyukan siyasa daban-daban.
Da yake waiwayen tarihin alaƙarsu ta siyasa, Kwankwaso ya ce alaƙar tasu ta samo asali ne tun shekarar 1993, lokacin da su biyun suka shiga harkar siyasa ƙarƙashin jagorancin marigayi Janar Shehu Musa Yar’Adua.