Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi hasashen cewa Arewa za ta bai wa Shugaba Bola Tinubu sama da kashi 70 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Yilwatda ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Abuja, yayin ƙaddamar da ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A), wadda ke yaƙin neman goyon bayan Tinubu da APC.
Ya ce ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Tinubu ke gudanarwa, musamman gine-ginen hanyoyi, layukan dogo da inganta kiwon lafiya, na daga cikin dalilan da za su sa ‘yan Arewa su sake zaɓensa.
Shugaban APC ya kuma ambaci naɗa ‘yan Arewa a muƙaman gwamnati a matsayin wani dalilin da ya kamata yankin ya goyi bayan wa’adin Tinubu na biyu.
Ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar da su mayar da hankali wajen tabbatar da nasarar Tinubu a rumfunan zaɓe a matakin ƙananan hukumomi da unguwanni.
Yilwatda ya ce idan magoya bayan APC suka tabbatar da nasara a rumfunan zaɓe na garuruwansu, za su iya cimma burin samun sama da kashi 70 cikin 100 na ƙuri’un Arewa.