Wata tsohuwar alƙaliyar Kotun Ƙoli ta Najeriya, Amina Adamu Augie, ta yi gargaɗin cewa cin hanci da rashawa a ɓangaren shari’a na lalata amincewar jama’a da kotuna, tare da mayar da su tamkar kasuwanni.
Augie ta bayyana hakan ne a Abuja yayin bikin cika shekaru 40 da kammala karatu na ɗaliban Makarantar Horar da Lauyoyi ta Najeriya ta shekarar 1986.
Ta ce cin hanci da rashawa da ke tattare da wasu alƙalai, lauyoyi da ma’aikatan kotu na raunana tsarin shari’a da kuma gurɓata martabar aikin lauya.
Tsohuwar alƙaliyar ta yi kira da a hukunta duk wanda aka samu da laifin rashin da’a, ba tare da la’akari da matsayinsa, tasirinsa ko girman aikinsa ba.
Ta kuma bayyana katsalandan ɗin siyasa, ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa da jinkirin shari’a a matsayin manyan matsalolin da ke addabar ɓangaren shari’a a ƙasar.
Augie ta jaddada cewa dawo da amincewar jama’a ba zai yiwu ta hanyar kamfen na inganta martaba kawai ba, sai an tabbatar da gaskiya da ladabtar da masu laifi cikin adalci.
Ta kuma yi gargaɗin cewa rashin samun cikakken ’yancin kuɗi na barazana ga ’yancin kotuna, tana mai cewa dogaro da bangaren zartarwa wajen samun kuɗin gudanarwa na iya raunana ’yancin shari’a.
Game da jinkirin shari’a, ta bayyana shi a matsayin wata babbar cuta da ke hana ’yan Najeriya samun adalci cikin lokaci da kuma kuɗin da za su iya biya.
Ta ba da misalin yadda wata ƙara kan ƙona awaki 12 ta kai har Kotun Ƙoli, duk da yawan shari’o’in da kotun ke fuskanta. Ta buƙaci a yi gyaran kundin tsarin mulki domin rage irin ƙarar da za ta iya kaiwa kotun, ta yadda za ta fi mayar da hankali kan muhimman batutuwan doka da kundin tsarin mulki.
Haka kuma, ta soki yadda wasu jami’an gwamnati ke ƙin bin umarnin kotu, inda ta kawo misalan tsare tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, da shugaban Harkar Musulunci a Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky, duk da umarnin kotu na a sake su.
Augie ta ce irin wannan hali na raunana ikon kotuna tare da aika saƙon cewa masu mulki za su iya yin watsi da doka.
Ta yi kira da a gudanar da cikakken gyara a tsarin shari’a, domin tabbatar da ’yancin kotuna, rage jinkiri, sauƙaƙa samun adalci da dawo da ƙa’idojin ɗabi’a a tsakanin lauyoyi da alƙalai.