Shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, bai goyi bayan miƙa mulki ga Bola Tinubu a 2023 da zuciya ɗaya ba, saboda yana ganin shugabancinsa zai iya zama matsala ga ƙasar.
Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a wani taron da Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta shirya, inda ya soki gwamnatin Tinubu kan yadda yake ganin tattalin arziki da yanayin rayuwar ’yan Najeriya suka tabarbare.
Ya ce furucin Tinubu na “Emilokan” a lokacin neman zaɓen 2023, wanda ke nufin “lokacina ne”, ya kamata ya sa ’yan Najeriya su yi tambayoyi kan manufarsa ta neman shugabancin ƙasa.
A cewarsa, Buhari ya yi tsayayya da matsin lambar wasu da suka dage sai Tinubu ne zai gaje shi.
Baba-Ahmed ya zargi gwamnatin Tinubu da gazawa a muhimman fannoni na ƙasa, yana mai cewa bai kamata burin mutum ɗaya ya jefa makomar Najeriya cikin haɗari ba.
Sai dai ya bayyana kwarin gwiwar cewa ’yan Najeriya za su shawo kan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, kamar yadda suka tsallake matsaloli a baya.
Ya kuma bayyana cewa jam’iyyun adawa na ƙoƙarin haɗa kai domin samar da ɗan takara guda da zai fafata da Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.