’Yan majalisar dokokin jihar Zamfara guda takwas da a baya suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar APC, sun sake jaddada amincinsu ga jam’iyyar da kuma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ne jagoranci ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara su takwas domin ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda suka sake jaddada biyayyarsu ga jam’iyyar APC da shugaban ƙasar.
‘Yan majalisar sun tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da kasancewa a APC, tare da nuna goyon bayansu ga shugaba Tinubu.
Bayan ganawar, Matawalle ya yi alƙawarin shigar da ’yan majalisar cikin ƙungiyar Tinubu Again Movement, domin su haɗa kai wajen tallata Tinubu da sauran ’yan takarar APC a zaɓe 2027.