NE

News Elementor

Adeleke ya tafi Abuja domin taron halartar ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na 2027

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bar jiharsa a wannan Laraba zuwa Abuja, gabanin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC na shekarar 2027.

A cikin wani bidiyo da ya haifar da cece-ku-ce a shafin X, an ga gwamnan yana tafiya tare da tawagarsa ta kula da harkokin zirga-zirga da ɗa’a zuwa wajen wani jirgin sama mai zaman kansa, wanda ake sa ran zai kai shi Babban Birnin Tarayya domin halartar taron.

An tsara gudanar da ƙaddamarwar ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

A kwanakin baya ne aka naɗa Adeleke a matsayin mai kula da ayyukan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Jihar Osun, domin yaƙin neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM