NE

News Elementor

Amurka Za Ta Riƙa Karɓa Gangar Mai Miliyan 50 Daga Venezuela-Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce nan ba da jimawa ba, Venezuela za ta riƙa bai wa Amurka gangar mai miliyan 50.
Wannan na zuwa ne bayan kama Shugaba Nicolás Maduro, wanda a halin yanzu ke fuskantar shari’a a birnin New York.

Tawagar ojojin Amurka na musamman ne suka mamaye Venezuela a ranar 3 ga Janairu, inda suka kama shugaban ƙasar da matarsa a wani samame da ya girgiza duniya tare da janyo suka da Alla-wadai daga ƙasashen duniya.

Bayan kama shugaban ƙasar ne, Trump ya sanar da cewa Amurka za ta jagoranci ƙasar ta Kudancin Amurka tare da mika ikon cibiyar man fetur ɗinta ga Amurka.

A wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta a ranar Laraba, Trump ya ce za a sayar da man da ake sa ran samu daga Venezuela, kuma kuɗaɗen da aka samu za a yi amfani da su ne domin amfanin al’ummar Venezuela da Amurka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM