NE

News Elementor

An kama ƴan ƙasashen waje da ake zargi da hannu a rashin tsaro a Najeriya – Bwala

Mai Bai wa shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa Labarai, Daniel Bwala, ya bayyana cewa dakarun sojin Najeriya sun kama wasu baƙin ƙasashe da ake zargin suna da alaƙa da matsalar rashin tsaro a wasu sassan ƙasar.

Bwala ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta The Link Up Podcast, inda ya ce gwamnati da sojoji sun ɓoye sunaye da ƙasashen waɗanda aka kama saboda dalilan tsaro da kuma ci gaba da hulɗar diflomasiyya da ƙasashensu.

Ya ce wasu ƙasashe na ƙoƙarin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Najeriya saboda muradun tsaro da tattalin arziki, ciki har da albarkatun mai.

Bwala ya kuma ce gwamnatin tarayya na ɗaukar matakan dakile yaɗuwar ayyukan Boko Haram da ISWAP daga Arewa maso Gabas zuwa Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, domin hana su isa Kudancin ƙasar.

Haka kuma, ya musanta zargin cewa sojoji na kare ‘yan ta’adda, yana mai cewa irin waɗannan zarge-zarge ba su da hujja. Ya ƙara da cewa an magance matsalolin rashin haɗin kai da a baya ke tsakanin Rundunar Soji da Rundunar Sojin Sama wajen gudanar da hare-haren yaƙi.

Dangane da gwamnatin Tinubu, Bwala ya yaba da abin da ya kira ci gaba a fannin tattalin arziki da kuɗaɗen ajiyar ƙasa, yana mai cewa ‘yan Najeriya ne za su yanke hukunci kan ko shugaban ya cancanci wa’adi na biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM