Rahotanni na cewa an kama Tsohon gwamnan jihar Anambra, Sanata Chris Ngige, a Abuja, Babban Birnin Tarayya.
An bs ds rshoton cewa jami’an tsaro dauke da makamai ne suka dauke shi daga gidansa da ke kan titin Justice Mohammed Bello a Abuja.
Har yanzu babu cikakken bayani game da kamun nasa kawo lokacin haɗa wannan rahoton.
Ba a san dalilin kamun ba, haka kuma ba a san wace hukumar tsaro ce ta dauki nauyin wannan aikin ba.
Babu wata hukumar tsaro da ta fitar da sanarwa a kan lamarin.
Tun da farko, wasu rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan, wanda ya kasance ministan Kwadago da Ayyuka a lokacin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, an yi garkuwa da shi a Abuja.
Amma wata majiya da ke kusa da Sanatan ta karyata batun garkuwar, ta bayyana cewa jami’an tsaro ne suka kama shi.
An kama Ngige ne kwanaki kadan bayan da aka kai hari kan jerin motocinsa a jihar Anambra.
Har ma an harbe Jami’in ɗan sanda ɗaya a lokacin harin, yayin da aka jikkata wasu da dama.
Ngige ba ya cikin motar da aka kai wa harin a lokacin, kuma har yanzu ba a kama kowa ba game da lamarin.