Jami’an tsaro sun kama wani mai suna Ashiru Abubakar, wanda ake zargi da kasancewa mai ba da bayanai ga ’yan bindiga da ke gudanar da ayyukansu a yankin Romo da ke ƙaramar hukumar Tambuwal a Jihar Sokoto.
Ana zargin Abubakar, wanda ya fito daga ƙauyen Gumfa Gebe da ke ƙaramar hukumar Wamakko, da haɗin gwiwa da ’yan bindiga a Tambuwal.
An danganta shi da wata barazana da aka yi wa mazauna Romo, inda aka buƙaci su biya Naira miliyan 10 ko kuma su fuskanci hari.
Da yake tabbatar da kama wanda ake zargin a ranar Laraba, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto (PPRO), Ahmed Rufai, ya ce an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.
Rufai ya ce kama wanda ake zargin da kuma gurfanar da shi a gaban kotu ya biyo bayan binciken da aka gudanar kan zargin alaƙarsa da wasu masu aikata laifuka.
Kakakin ’yan sandan ya ce rundunar za ta ci gaba da ƙarfafa matakan da take ɗauka domin dakile ayyukan mutanen da ke taimaka wa masu aikata laifuka a jihar.