NE

News Elementor

An kama yansandan da suka karbi cin hancin N53,000 daga shugaban ICPC a Abuja

Rundunar yansandan birnin Abuja ta kama wasu yansanda 4 da ake zargi da karbar cin hanci na naira 53,000 a hannun shugaban hukumar yaki da rashawa ta ICPC, Dr Musa Aliyu, a wani shingen bincike da suka kafa a birnin Abuja.

Yansandan, wadanda rahotanni ke cewa ba su san wanda suka kama shi ne shugaban hukumar yaki da rashawa ba, sun tilasta ma Aliyu ciro kudin daga wani shagon POS kafin ya mika musu domin su raba a tsakaninsu.

Kwamishinan yansandan birnin Abuja, Ahmed Sanusi ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Abuja, inda ya bayyana jami’an a matsayin yan ta’adda wadanda rundunar yansandan Nigeria ba za ta iya aiki da su ba.

A cewar Sanusi, yansandan sun yi watsi da aikin da aka basu, inda suka kafa shingen bincike a yankin Banex dake unguwar Wuse, suna tare motoci suna yi musu bincike da karbar kudi.

Ya ce shugaban na ICPC ya fada tarkonsu ne lokacin da suka tare shi tare da neman ya biya su kudi kafin ya wuce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM