Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da naɗin Lawan Ahmed Mohammed, PhD, a matsayin sabon Sarkin Gumel na 17, bayan rasuwar tsohon Sarkin Gumel, marigayi Alhaji Ahmad Muhammad Sani II, CON.
Sakataren gwamnatin jihar Jigawa Bala Ibrahim ne ya sanar da nadin.
Marigayi Sarkin Gumel ya rasu ne a ranar 3 ga Agusta 2026 a ƙasar Masar, bayan fama da rashin lafiya na kimanin makonni shida, lamarin da ya jefa masarautar da al’ummar Gumel cikin jimami.
Sabon Sarkin, Lawan Ahmed Mohammed, ɗan fari ne ga marigayi Sarkin Gumel na 16, kuma ya taso cikin al’adun masarautar Gumel, inda ya samu tarbiyyar da ta ginu kan ladabi, hikima, adalci da hidima ga al’umma.
Ya yi karatun digiri na farko a fannin Lissafi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sannan ya samu digirin biyu na MSc a Computing daga De Montfort University da ke Birtaniya da Operations Research daga Universiti Putra Malaysia. Daga bisani ya samu digirin digirgir, PhD, a Computer and Communication Systems Engineering daga jami’ar ta Malaysia.
Kafin naɗinsa, sabon Sarkin ya yi aiki a fannin ilimi da fasahar sadarwa a ƙasashe daban-daban, ciki har da Malaysia da Saudiyya, inda ya jagoranci sashen Computer Science and Engineering a Jami’ar Hafr Al-Batin. A Najeriya kuma, ya taɓa riƙe muƙamin Daraktan CyberSecurity a Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa, NITDA.
Lawan Ahmed Mohammed, wanda ya wallafa tare da haɗa hannu wajen wallafa sama da 40 na binciken kimiyya, yanzu zai jagoranci masarautar Gumel a wani sabon babi da ake sa ran zai mayar da hankali kan ilimi, haɗin kan al’umma, matasa, fasaha, bunƙasar tattalin arziki da kuma kare al’adun masarautar.