Yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun tsaurara matakan tsaro a fadin kasar nan a yayin da ake saura kwana 5 a gudanar da bukin Kirsimeti.
Daruruwan yan Nigeria ne ke tafiye-tafiye zuwa garuruwansu na asali domin gudanar da bukin, wasu a mota wasu kuma a jiragen sama.
To saidai, yanayin sufurin sama ya yi tashin gwauron zabi a wannan shekara lamarin da ya sa mutanen da suka saba hawa jirgin sama suka koma amfani da motoci wasu kuma suka hakura da tafiyar tasu.
Rahotanni daga sassa daban-daban na kasar nan sun tabbatar da cewa, an samu karuwar zirga-zirga daga yankin kudu maso yamma da arewacin zuwa zuwa sassan kudu maso gabas da kudu maso kudu.
Kazalika bayanai sun ce an tsaurara matakan tsaro domin dakile masu yunkurin amfani da wannan lokacin wajan gudanar da ayyukan ta’addanci.