NE

News Elementor

An yanke wa shugaban RSF hukuncin ɗaurin rai da rai a Sudan

Wata kotu a jihar Port Sudan, da ke ƙasar Sudan ta yanke wa jagoran RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, da aka fi sani da ”Hemedti”, hukuncin ɗaurin rairai da rai.

A wata shari’a da aka yi a bayan Hemedti, wanda bai halarci kotun ba, an same shi da laifin aikata kisan ƙare dangi da laifukan yaƙi da laifukan jin ƙai da kuma hare-hare kan fararen hula.

Hukuncin kotun da aka yanke ranar Lahadi 12 ga watan Yulin 2026, shi ne mafi girma da aka yi wa jagoran na RSF tun bayan fara yaƙin a 2023.

Shari’ar ta mayar da hankali ne kisan da aka yi w gwamnan Yammacin Darfur, Khamis Abbakar, a shekarar 2023.

An zargin garkuwa da shi sannan aka kashe shi bayan da ya zargi dakarun RSF da aika kisan ƙare dangi.

Hukuncin ya kuma haɗa da wasu manyan jami’ar RSF, ciki har da ƴan’uwan Hemedti, Abdelrahim Dagalo da Algoney Dagalo, duk a bayan idonsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM