
Aƙalla mutane 25 ake fargabar sun mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya auku a ƙaramar hukumar Nguru ta Jihar Yobe, yayin da rahotanni suka nuna cewa an ceto fasinjoji 13, sannan wasu 14 har yanzu ba a gano inda suke ba, kamar yadda wani rahoton farko daga hukumomi ya bayyana.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:48 na yammacin ranar Asabar, lokacin da wani kwale-kwale da ke ɗauke da fasinjoji 52 ya kife a yayin da yake tafiya daga garin Adiyani da ke ƙaramar hukumar Guri ta Jihar Jigawa zuwa garin Garbi da ke haramar hukumar Nguru ta Jihar Yobe.
Shaidun gani da ido da kuma binciken farko sun nuna cewa waɗanda hatsarin ya rutsa da su suna dawowa ne daga garin Adiyani, inda suka je yin kamun kifi da noma da sauran harkokin kasuwanci, kafin kwale-kwalen ya kife ana tsaka da tafiya.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Yobe ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin babban sakataren gudanarwarta.