
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana ƙarara cewa makomarsa ta siyasa za ta lalace gaba ɗaya idan Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya samu damar yin wa’adi na biyu a kan mulki, lamarin da ke nuna ƙara tsananta rikicin siyasar da ya daɗe yana addabar jihar mai arzikin man fetur.
Mista Wike ya faɗi hakan ne a ranar Asabar yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Ƙaramar Hukumar Okrika ta Jihar Rivers, inda ya gana da shugabannin jam’iyya, magoya bayansa da abokan siyasa, a daidai lokacin da rikici ke ƙara kamari tsakaninsa da magajinsa.
Cikin kakkausar murya, tsohon gwamnan Jihar Rivers ya ce tuni an yanke shawara da ta dace game da zaɓen gwamna na shekarar 2027, yana mai jaddada cewa barin Mista Fubara ya samu wa’adi na biyu zai zama kamar kashe kansa ta fuskar siyasa, shi da mutanensa.