NE

News Elementor

Babban Bankin CBN Ya Amince Da Biyan Kudin Guzuri Ga Alhazzai A Wannan Shekara

Babban bankin Nigeria, CBN, ya amince da biyan kudin guzuri ga alhazzan Nigeria a wannan shekara, inda ya amince da dage aiwatar da tsarin biyan kudin ta internet har zuwa shekara mai zuwa.

Amincewar na zuwa ne bayan tattaunawa da jami’an hukumar NAHCON, karkashin jagorancin Amabassador Ismail Abba Yusuf suka gudanar, domin magance damuwar da alhazzai da masu ruwa da tsaki ke nunawa kan batun sauya tsarin biyan kudin na guzuri daga bada kudi hannu zuwa bada kati.

A wata wasika da sashen kula da kudi na bankin ya fitar, CBN ya ce ya amince da bayar da guzuri na kudi hannu da alhazzan wannan shekara, amma kuma hakan ya takaita ne a iya shekarar nan da muke ciki.

To sai dai, bankin ya jaddada cewa zai ci-gaba da shirinsa na aiwatar da tsarin biyan kudin na zamani, tare da cewa daga shekara mai zuwa, za a biya kudin guzurin ne ta hanyar katin cirar kudi.

Ya kuma umarci hukumar ta NAHCON ta fara wayar da kan alhazzai game da hanyoyin biyan kudin ta na’ura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM