Bayan gagarumin rinjayen da jam’iyyar adawar Bangladesh ta samu a zaɓen ƙasar, bayanai na nuna Shugabanta Tarique Rahman, ya zama sabon firaministan ƙasar.
Kwanaki biyu kafin a kaɗa ƙuri’ar zaɓe, Rahman ya shaidawa kamfanin dillancin labaran faransa AFP cewa shakka babu ya na da yaƙinin cewa jam’iyyarsa da hamɓararriyar shugaba Sheikh Hasina ta danne tsawon shekaru 15 za ta dawo da ƙarfinta, a ƙasar mai yawan mutane miliyan 170 a yankin kudancin Asia.
Shi ma Sakataren hukumar zaɓen Bangladesh Akhtar Ahmed ya shaidawa manema labarai cewa sakamakon da hukumar ta fitar na nuna cewa BNP ta lashe kujeru 212 na majalisar ƙasar, yayin da ƙawancen jam’iyyar ƴan uwa musulmi ta samu kujeru 77.
Wani babban jagora a jami’yyar ta BNP, Ruhul Kabir Rizvi ya yi ikirarin cewa nasarar da su ka yi ba ta misaltuwa la’akari da yadda suka lashe kaso sama da 2 cikin 3 a majalisar ƙasar.Kaso 59 cikin 60 na masu kaɗa ƙuri’a ne aka samu a zaɓen raba gardamar da ta gudana a ƙasar.