NE

News Elementor

Yan Ta’adda Sun Fara Tura Sakonnin Gargadi Ga Kauyuka Da Dama A Jihar Kwara

Rahotanni sun ce a cikin kwanaki 6 da suka gabata, yan ta’addan sun aike da sakonni zuwa kauyuka 4 tare da barazanar kai musu farmaki daga yanzu zuwa kowane lokaci.

Manema labarai sun gano cewa, an ajiye wata wasika a kauyen Ira dake tsakanin Inaja da Aho a karamar hukumar Oyun.

Tun farko yan bindigar sun tura wasikar gargadi ga kauyen Dunshigogo a karamar hukumar Kaiama, kwanaki kadan bayan harin ranar 3 ga watan Fabrairu a kauyen Woro wanda ya haddasa mutuwar mutum fiye da 176 da sace wasu 38.

Bugu da kari, bayanai sun ce mazauna Ira, Inaja da Aho sun fara yin hijira daga garuruwan nasu sakamakon barazanar da yan ta’addan ke yi.

Wani basarake a kauyen Ira, wanda ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce an ajiye wasikar ce a wata tashar babura dake kusa da babban masallacin kauyen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Recent News

Trending News

Editor's Picks

Gwamnan Kano Abba Kabir ya tura sunan mai magana da yawunsa, Sanusi Bature zuwa majalisa domin naɗa shi kwamishina

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunayen mutane biyu ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni, ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa. Sannan an miƙa sunan Hon. Balarabe Sa’idu Gani. Ana sa ran Majalisar za ta tantance mutanen biyu a ranar Talata,...

NE

News Elementor

Popular Categories

Must Read

©2025 – All Right Reserved. IconicFM