Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alheri Attahiru Bafarawa, ya nesanta kansa da ga batun komawa jam’iyyar APC mai mulki.
Bafarawa ya shaida wa BBC cewa shi da ma kowa ya san ya yi ritaya daga siyasa, a don haka batun ya koma APC sam ba shi da wannan niyyar.
Ya ce, Idan za a iya tunawa ya ce ya bar siyasa ko ta zabe ko ta nadi, kuma babu wata jam’iyya da zai shiga, amma zai shiga kungiyar taimakawa matasa da sauransu.
Attahiru Bafarawa, ya yi wannan kalamai ne bayan da dubban magoya bayansa suka koma jam’iyyar APC a jiharta Sokoto, sakamakon abin da suka kira gamsuwa da kamun ludayin mulkin gwamnan jihar Ahmad Aliyu.
